Fitacciyar jaruma a cikin shirin Dadin Kowa Fati Nayo, wacce aka fi sani da sunan Kyauta Dillaliya, ta bayyana burin da ta ke da shi dangane da irin mijin da take so ta aura a duk lokacin da Allah ya kawo mata mijin aure.
Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin Dimukaradiyya lokacin da ya ke tamabayar ta, burin ta da ta ke so ta cimma a nan gaba, tun da ta zama babbar Jarumar da duniya ta san ta.
In da ta ke cewa “Babban burin da na ke da shi a yanzu shi ne, Allah ya kawo mun mijin aure, wanda zai kasan ce mai addini, kuma mai tsafta ba irin kazaman mazan nan ba, domin ni ina son mutum mai tsafta ba kazami ba.”
Ta ci gaba da cewa “Ni a matsayina na mace musulma da ta taba yin aure har da ya’yan biyu, ba zan so na kare rayuwata a yanzu ba ni da aure ba, don haka ina fatan Allah ya kawo mun mijin aure wanda zai kasan ce abokin zaman aure, da mu ke son juna tsakani da Allah.”
Mun tambaye ta ko za ta auri miji kamar Kamaye wanda a yanzu shi ne mijin ta a cikin shirin Dadin Kowa?
Sai ta yi dariya ta ce”Ai wannan a cikin Dirama ne, amma a zahiri Baba Kamaye Kakana ne, don haka ina kallon sa a matsayin Ubangida ne a waje na, ka ga ba maganar aure a tsakanin mu. ”
To ko wanne miji Kyauta Dillaliya ta ke son ta aura wanda za su yi zaman aure da shi?
Sai ta ce” Ina son na auri mijin da mu ke kusan kamar shekaru daya da shi. Yanzu ka ga ban fi shekara 45 ba, don haka ina son mijin da zan aura ya zama shekarun mu daya da shi, wanda hakan zai ba mu damar mu yi zama na soyayya da shi. ” Inji ta
A karshe ta yi kira ga abokan sana’ar ta da cewar, duk wata harka da za su yi, to kada ta dauke musu hankali dangane da aure, domin shi ne mutuncin mace da rufin asirin ta.
