Za Mu Kafa Gwamnatin Riko Nan Da Makwanni Biyu – Sojojin Guinea


A kasar Guinea, jagoran sojojin da suka hambarar da gwamnatin shugaba Alpha Conde, ya sanar da cewa za su kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya cikin makonni masu zuwa.

Laftanal kanar Mamady Doumbouya ya shaida wa mambobin tsohuwar gwamnatin cewa ba za a muzgunawa kowa ba.

Sai dai ya shaida wa ministocin gwamnatin cewa ba za a barsu su fita daga kasar ba, kuma ya bukaci su mika motocin gwamnati da ke hannayensu ga sojojin kasar.

Shugaba Alpha Conde mai shekara 83, wanda sojojin ke tsare da shi a yanzu – a bara ya tsawaita mulkinsa inda ya so ya jagoranci kasar a karo na uku.

Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka sun yi Allah-wadai da juyin mulkin.

Related posts

Leave a Comment