Ministar Harkokin Ku?a?e Zainab Ahmed ta bayyana cewa har yanzu bashin da Najeriya ke ciwowa bai kumbura mata cikin da zai iya fashewa ba.
Ministar ta ce har yanzu Najeriya ba ta tsallake ?a’idar Gejin Tattalin Arzikin Cikin Gida na ba, inda ta ce har yanzu bashin bai wuce kashi 23 bisa 100 ba.
Zainab ta yi wannan bayani ga manema labarai a Abuja a ranar Litinin.
Cikin makon jiya ne Hukumar ?ididdigar Al?aluman Bayanai ta ?asa (NBS) ta bayyana malejin Tattalin Arzikin Cikin Gida (GDP) ya ?aru zuwa kashi 5.01 a watannin Afrilu, Mayu da Yuni na 2021.
Zainab ta ce ai babu wani abin damuwa, domin ku?a?en da ake rantowa ana yin ayyukan raya ?asa ne da su, wa?anda su ka ha?a da aikin lantarki, titina, samar da ruwa da titinan jiragen ?asa, wa?anda su ne ?ashin bayan inganta tattalin arziki.
“Mu na ciwo bashi a cikin yin taka-tsantsan ?in da har yanzu ba mu wuce kashi 23 na Gejin Ma’aunin GDP ba.
“Na sha fa?a ba sau ?aya ko sau biyu ba cewa babbar matsalar ?asar nan ita ce ?arancin ku?a?en shiga, wa?anda ?arancin na su ke sa tilas a ke ciwo basussuka domin a yi ayyukan raya ?asa da inganta tattalin arzikin cikin gida.”
Kwanan baya ne Majalisar Tarayya ta damu da tulin bashin da Gwamnatin Tarayya ke ciwowa, alhali hukumomi ba su zuba ku?a?en shiga asusun Gwamnanti.
Kwamitin Lura da Ku?a?en Gwamnantin Tarayya na Majalisar Tarayya ya nuna ?acin rai ganin yadda Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari za ta ciwo bashin naira tiriliyan 5.62 domin narkawa a yi ayyukan raya ?asa a kasafin 2021, amma kuma a gefe ?aya hukumomin Gwamnantin Tarayya da yawa sun ri?e ku?a?en shiga sun ?i zubawa a cikin Asusun Gwamnantin Tarayya domin a samu ku?a?en yin ayyuka.
Shugaban Kwamitin Ku?a?e na Majalisar Tarayya James Feleke ya ce, “a gaskiya ba mu jin da?in yadda wasu hukumomin gwamnati ke ri?e ku?a?e ba su zubawa cikin asusun Gwamnanti, ita kuma gwamnati an bar ta fita gaganiyar ciwo basussukan da za ta yi ayyukan raya ?asa.
“Don Allah ya zama wajibi mu tashi mu nuna kishin ?asar mu don mu ci moriyar bun?asar ta baki ?ayan mu.”
Feleke ya magana ne ganin yadda wasu hukumomin Gwamnantin Tarayya su ka kasa bada bayanai wasu kuma su ka ?i zuba ku?a?en shigar su a Asusun Gwamnantin Tarayya tsawon lokaci.
Kwamitin dai na gayyatar Hukumomi ne ?aya bayan ?aya su na gabatar da bayanan ku?a?en shigar da su ke tarawa duk shekara, domin a ji yadda za a yi kirdadon ku?a?en shigar da za su tara daga shekarar 2022 zuwa 2024.
“?aya daga cikin matsalar ?asar nan ita ce rashin wadattattun ku?a?en shiga a aljihun gwamnatin tarayya. Dalili kenan Majalisar Tarayya ke son sanin adadin ku?a?en shigar da kowace hukuma ke tarawa a kowace shekara.” Inji Feleke
“Wasu ayyuka da dama da hukumomin gwamnati ke yi duk kashe ma?udan ku?a?e ne kawai ake yi a hanyar da ba ta cancanta ba. Kamata ya yi su daina bayar wa?annan manyan ayyuka na manyan kwangiloli, su maida hankali wajen tara wa Gwamnatin Tarayya ku?a?en shiga kawai.
Daganan Feleke ya juya wajen Hukumar Sadarwa ta ?asa (NCC), inda ya umarce ta cewa ta gabatar da bayanan ku?a?en da ta tara tun daga shekarun 2018, 2019 da 2020.
