Jam’iyyar APC Ta Yaba Juriyar ‘Yan Najeriya

Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC mai mulki ta sanar da cewa ta yanke hukuncin kafa kwamitin kasafi da sauran kwamitoci gabanin babban taronta na ?asa a watan Fabrairu.

Da yake jawabi ga manema labarai jim ka?an bayan taron kwamitin rikon kwarya, sakataren APC na ?asa, Sanata James Akpanudoedehe yace Jam’iyyar ta yaba da jinjina wa juriya da hakurin ‘yan Najeriya, sannan kwamitinsu ya sake nazari kan ayyukan da ya gudanar tsawon shekara daya.

A baya-bayan nan ne jiga-jigan APC na ?asa suka gana da shugaban ?asa Muhammadu Buhari, a gidan gwamnatinsa Aso Rock, kan wasu kalubale da Jam’iyyar ke fuskanta a jihohi.

Yayin wannan ganawa ta su ne, suka amince da cewa za’a gudanar da babban taron APC na ?asa a watan Fabrairu, amma ba su za?i rana ba.

Kazaika a taron kwamitin (CECPC) ?ar?ashin jagorancin gwamna Mala Buni, ya gaza sanar da ainihin ranar da taron zai gudana a watan Fabrairu.

“A taron kwamitin rikon kwarya (CECPC) na APC karo na 18 da ya gudana a sakateriyar jam’iyya ta ?asa ranar 20 ga watan Disamba ya yi duba zuwa ga ayyukan da ya gudanar tsawon shekara ?aya.”

“Kwamitin ya kuma tattauna kan batutuwa da dama kuma ya cimma matsaya kamar haka: Game da taro na ?asa an yanke kafa kwamitin kasafin kudi da sauran kwamitin da suka shafi taron.”

Related posts

Leave a Comment