Kyaftin din Real Madrid ya tsawaita yarjejeniyarsa domin ci gaba da kasancewa da kungiyar ta Bernabeu har zuwa shekara ta 2023.
Hakan shi zai sa dan kwallon ya kasance a Real na tsawon shekaru 14.
Benzema, mai shekaru 33, ya je Real Madrid ne a shekara ta 2009 inda ya zura kwallo 281 kawo yanzu.
Dan wasan na Faransa shi ne na biyar a cikin jerin masu yawan zura kwallo a Real.
Sabunta kwangilar ta yi daidai ta matakin da golan Belgium, Thibaut Courtois wanda ya tsawaita kwangilar har zuwa shekarar 2026
