Tsohon hadimin Shugaban ?asa kan harkokin majalisa, Abdurrahman Kawu- Sumaila ya baiyana cewa zamanin ?a?aba ?an takara a siyasar Nijeriya ya wuce.
Kawu-Sumaila ya kuma baiyana cewa ya kamata jam’iya mai mulki, APC ta ?auki darasi a kan za?en gwamna na Anambra, inda ?an takarar jam’iyar APGA, Charles Soludo ya lashe za?en.
Kawu-Sumaila ya yi wannan kira ne a wani sa?o da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Asabar.
A sa?on da ya wallafa, tsohon wakilin Takai da Sumaila a majalisar wakilai ta tarayya ya ce shi bai damu da za?en fidda gwani na ?ar-tin?e ko akasin hakan a APC.
“Ni ban damu da za?en fidda gwani na ?ar-tin?e ko akasin hakan a APC ba. Amma dai, ya kamata mu fa?awa kan mu gaskiya. Zamanin ?a?aba ?an takara ya wuce. Za?en Anambra dai ya kamata ya zame mana izina,” in ji Kawu-Sumaila
