Rahotanni daga birnin Kano na bayyana cewar Fitaccen jarumin masana’antar Kannywood, gwanin rawa da waka, Garzali Miko ya shirya tsaf zai angwance da masoyiyarsa mai suna Habiba.
Kamar yadda jarumin tare da sauran abokan aikinsa suke ta wallafawa a shafukansu na Instagram, jarumi Garzali Miko zai aura masoyiyarsa ne a ranar Juma’a mai zuwa.
Kamar yadda katin daurin auren ya bayyana, za a daura auren jarumi Garzali Miko da Habiba Umar Ahmda Dikwa da karfe 1 da rabi na ranar Juma’a.
Za a daura ne garin Kaduna a anguwar Rigasa a cikin Masallacin Fajrul Islam.
