Dakataccen Shugaban Hukumar Ya?i da Cin-hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, ya sha?i iskar ?anci bayan da ya cika sharu??an beli.
Rahotanni sun bayyana cewa tuni Rimingado ya isa gida wajen iyalinsa a ranar Asabar.
Wata Kotun Majistare, ?ar?ashin Babban Majistare Aminu Gabari ce ta bada belin Rimingado bayan da s ka gurfanar da shi karo na farko a ranar Juma’a.
A tuna cewa a ranar Alhamis ne dai wasu ?an sanda ?auke da makamai su ka cafke Rimingado a masaukin gwamnatin Sokoto, yayin da ya je tantancewa a kan takarar sa ta gwamna.
A na tuhumar Rimingado ne da laifin bada bayanan ?arya, laifin da ya sa?a da sashe na 149 na kundin dokoki na jihar Kano na 2019.
