Mun Dukufa Wajen Ceto Fasinjojin Jirgin Abuja – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya bada tabbacin kokarin gwamnatin shi na ganin an ceto dukkanin Fasinjojin Jirgin kasa da ‘yan bindiga suka sace a hanyar Abuja ba tare da samun matsala ba.

Shugaban ya umurci hukumomin tsaro da su tabbatar da ceto wadanda lamarin ya rutsa da su, ta kowane hali amma tare da yin taka tsantsan wajen kare rayukan su.

A ranar 28 ga watan Maris ne ‘yan ta’adda suka kai hari kan wani jirgin da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, inda suka kashe akalla mutane tara tare da raunata wasu da dama, da kuma yin awon gaba da fasinjojin da ba a san adadinsu ba.

Shugaba Buhari, wanda ya tabbatar da cewa, ana ci gaba da kokarin ganin an dawo da duk wadanda ‘yan ta’adda ke tsare da su lafiya, ya ce gwamnati za ta binciko duk wata dama da za ta samu wajen ganin an ceto wadanda aka yi garkuwa da su, a raye.

Ya umurci hukumar kula da layin dogo ta Najeriya (NRC) da ta samar da karin bayanai na yau da kullum ga iyalan wadanda aka sacen.

A cewar Shugaban, ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan ba kamar kwararrun sojoji bane, ba sa mutunta ka’idojin yaki kuma suna iya illata wadanda suka yi garkuwa da su idan aka kai musu hari.

Shugaba Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su samar da yanayi na kyama ga ‘yan ta’adda dake boye a cikin al’umma. Shugaban ya ce hada karfi da karfe tsakanin jami’an tsaro da al’ummomi ne zai kawo gagarumin sauyi wajen murkushe ‘yan ta’adda da ta’addanci a kasar.

Related posts

Leave a Comment