Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya jadadda biyayyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyar APC yayin da yake shirin neman shugabancin kasar a 2023.
Wata sanarwa daga ofishin watsa labaransa ya fitar ya ce Amaechi ya yi bayani ne a lokacin wata ganawa da shugabanni, wakilai da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a sakatariyar APC ta jihar Ribas a ranar Juma’a.
Ya bayyana cewa a yunkurinsa na son zama shugaban kasar Najeriya wanda ya cancanci hawa kujerar, bai kasance mai gaggawa ko rashin biyayya ba. Amaechi ya yi bayanin cewa abun bakin ciki ne cewa yan siyasa da dama basu fahimci manufar biyayya ba.
Ya yi ikirarin cewa idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanke shawarar zabar wani daban a matsayin dan takarar shugaban kasa a maimakon shi, zai marawa mutumin baya ko wanene.
“Biyayya ba shine idan ba a zabe ka ba, sai ka bijire; biyayya na nufin ka bi mutumin da ke jagorantarka. Ni mutum ne mai biyayya sosai kuma wadanda basa biyayya, ina musu fatan alkhairi; wadanda ke son yin duk abun da suke son yi, ina masu fatan alkhairi.
“Za a ba kowa dama; za mu yi takarar wannan zabe na shugaban kasa; za mu yi takara, kuma ina biyayya ga shugaban kasa kuma ina biyayya ga jam’iyya, duk abun da jam’iyya ta zaba, zan mara masa baya.
