Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa Malam Abdulsalam Abubakar, mahaifin daliba yar shekara biyar, Hanifa, wanda shugaban makarantarsu ya kashe, ya kai ziyarda sakatariyar kungiyar yan jarida, NUJ, na Kano a ranar Juma’a don godiya kan rawar da kafar watsa labarai ta taka wurin ganin an yiwa yarsa adalci cikin gaggawa.
Ya ce ba za a iya kwatanta muhimmancin rawar da kafafen watsa labarai suka taka ba wurin ganin an yi adalci ga yarsa da wasu suka kashe. Abubakar ya ce: “Kafafen watsa labarai sun tabbatar an yi adalci ba tare da bata lokaci ba, yayin shariar, an samu makasan da laifi, an kuma yanke musu hukunci.
“Ina tunanin babu kalaman da zan iya amfani da su wurin gode wa yan jaridan Najeriya saboda bibiyar labarin kisar ‘ya ta, daga ranar da aka kashe ta har ranar da aka yanke hukunci. “Za mu dade ba mu manta abin da kuka yi min da iyali na ba, abin da zan kara kawai, shine Allah ya saka muku da alheri saboda sauke nauyin aikinku.
Dalilin ziyara ta shine gode wa yan jarida bisa rawar da suka taka don ganin an kama wadanda suka kashe ‘ya ta kuma sun girbi abin da suka shuka.”
