Siyasa: APC Ta Tafka Asara A Abia

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Abia na bayyana cewa Jigo a jam’iyyar APC, a jihar Cif Princewill Ukaegbu ya fice daga jam’iyyar ya koma Action Peoples Party, APP.

Ana sa ran Ukaegbu, tsohon shugaban karamar hukumar Umuahia ta Arewa zai sanar da sauya shekarsa nan ba da dadewa ba a hukumance.

Sanarwa daga dan takarar gwamnan na APP a jihar, Cof Mascot Uzor Kalu, ta ce jigon na APC dan siyasa ne mai kusanci da talakawa kuma sauya shekarsa za ta taimaka masa wajen samun nasara.

Wani sashi na sanarwar ta ce: “Mascot yana kara fice a takarar gwamna. Zabe ne tsakaninsa da sauran. A zamanin gwamnatin Orji Uzor Kalu kawai aka samu gwamnati mai kyau. Abin da muke da shi yanzu wasan kwaikwayo ne. Lokaci ya yi da za a dawo wa jihar da darajarta.”

Ficewar ta Ukaegbu na zuwa ne kwanaki kadan bayan shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu ya fada wa shugabannin jam’iyyar na jihar Abia su daidaita kansu gabanin zaben 2023.

Related posts

Leave a Comment