Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Oisnbajo ya tafi Accra babban birnin ?asar Ghana domin wakiltar Shugaba Muhammadu Buhari a wani taro na musamman da ?ungiyar Bun?asa Tattalin Arzikin ?asashen Yammacin Afrika wato ECOWAS ta shirya.
Mai magana da yawun mataimakin shugaban ?asar Laolu Akande ne ya fitar da sanarwar inda ya ce shugabannin ?asashen yammacin Afrika za su tattauna a yayin taron kan batun siyasar ?asar Mali.
Osinbajon ya tafi tare da ?aramin ministan harkokin waje na Najeriya Ambasada Zubairu Dada, haka kuma ana sa ran za su dawo a yau Lahadi.
Ko a Nuwambar bara sai da Mista Osinbajo ya je Accra domin tattaunawa kan wannan batu na siyasar Mali da kuma ?asar Guinea.
Daga bisani kuma mai shiga tsakani na ?ungiyar ta ECOWAS Goodluck Jonathan ya tafi Mali a ranar 5 ga watan Janairun 2022 domin tattaunawa da hukumomin ?asar Mali kan batun jadawalin mi?a mulki ga farar hula.
A yau ne gwamnatin sojin ta Mali ta ce ta mi?a sabon jadawalin ga ?ungiyar ta ECOWAS gabannin soma taronta.
