Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan Imo Rochas Okorocha, kuma ?an takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.
EFCC ta tafi da Rochas daga gidansa da ke unguwar Maitama a Abuja da yammacin Talata.
Jami’an EFCC da ?an sanda sun yi dirar mikiya tare da mamaye gidan tsohon gwamnan, inda rahotanni suka ce an yi harbi a ?o?arin kama shi.
Hukumar EFCC ta ce matakin ya biyo bayan ?in amsa gayyatar da tsohon gwamnan ya yi bayan tsallake belin da ya samu a farko.
A ranar 24 ga watan Junairun shekarar 2022 ne EFCC ta shigar da kara a gaban kotu tana tuhumar Okorocha da laifuka 17 da suka hada da karkatar da kudaden al’umma da kadarori da suka kai naira biliyan 2.9.
Hukumar ta ce yun?urin gurfanar da Sanata Okorocha sau biyu ya ci tura sakamakon ?in amsa gayyatar da aka yi ma shi.
