Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Honorabul Abdulmumin Jibrin yana da ra’ayin cewa Abdullahi Umar Ganduje bai yi nasara a zaben Gwamnan jihar Kano a 2019 ba Tsohon ‘dan majalisar yace Rabiu Kwankwaso da mutanensa na PDP suka lashe zaben Gwamna, amma a karshe APC ta zarce.
A tattaunawar da gidan talabijin na Channel ya yi da shi bayan mukamin da Kwankwaso ya bashi na mai magana da yawun sa, Abdulmumin Jibrin ya tabo batutuwan da suka shafi gwamnati da siyasar kasa.
Da yake amsa tambaya a game da makomar Sanata Ibrahim Shekarau a NNPP, Jibrin ya nuna ko Sanatan ya sauya-sheka, jam’iyyarsu za ta kai labari a 2023.
Kakakin kwamitin neman takarar na NNPP yana cewa babu wani wanda zai iya kada NNPP. Kwankwaso ya rike siyasar Kano Tsohon ‘dan majalisar yace a 2019 an ga aya a zaben Kano, inda duk manyan ‘yan siyasa suka tare a APC, amma Rabiu Kwankwaso ya nuna masu nauyinsa.
“A 2019, abin takaici, dukkaninmu sai mu ka bi Ganduje, Shekarau, Kabiru Gaya, Barau Jibrin, Kawu Sumaila, duk wani babba a Kano ya bi Ganduje, Meya faru? Kwankwaso shi kadai a gefe guda, ya doke mu a zaben Gwamna.
