Yakin Rasha Da Ukraine Zai Jefa Najeriya A Tasku – Bankin Bada Lamuni

Bankin bada lamuni na duniya IMF ya bayyana cewa Najeriya da sauran kasashen Afrika na cikin halin barazanar tashin farashin kayan abinci, da man fetur sakamakon yakin dake gudana tsakanin Rasha da Ukraine a halin yanzu.

Darakta Manaja na IMF, Ms Kristalina Georgieva, ta bayyana hakan bayan ganawa da Ministocin kudin kasashen Afrika, gwamnonin bankuna kasa, wakilan majalisar dinkin duniya don tattauna illar da yakin Ukraine ka iya wa nahiyar Afirka.

“Yakin Ukraine na lalata rayukan miliyoyin mutane kuma yana gurgunta tattalin arzikin Ukraine. “Wannan na da illa ga Afrika.

Mun tattauna yadda Afrika zata farfado. Afrika na fuskantar barazanar yakin Ukraine ta hanyoyi hudu – tashin farashin abinci, tashin farashin mai, rashin kudin shiga na yawon ganin ido, da kuma wuya samun harkalla da sauran kasashe.”

A cewarta, asusun IMF shirya yake da taimakawa kasashen Afrika wajen dakile illolin yakin ta hanyar samar da tsare-tsare na shawari da bashi.

Related posts

Leave a Comment