Rahoton dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Jami’ar Greenfield ta koma matsuguninta na cikin garin Kaduna bayan yan bindiga sun kai hari a harabar makarantan na dindindin da ke babban hanyar Kaduna zuwa Abuja a watan Afrilun 2021.
Kimanin dalibai da malamai 23 ne aka sace yayin harin da yan bindigan suka kai yayin da dalibai biyar suka mutu a hannun yan bindigan daga bisani cikin daji.
Shugaban jami’ar, Farfesa Simon Daniel Katung yayin bikin daukan dalibai karo na 4 ya gargadi dalibansa su daina wallafa bayanai game da makarantar a soshiyal midiya. Ya bukaci daliban su rika takatsantsan da tsaronsu sannan su daina tafiye-tafiyen dare.
Ya tabbatarwa iyayen yara cewa makarantan a shirye ta ke don yaye dalibai da za su iya gogayya da takwarorinsu na kasashen duniya. Katung ya yi gargadin cewa makarantar ba za ta amince da ayyukan kungiyar asiri ba yana mai cewa nan take za a kori duk wanda aka samu da aikata hakan.
“Jami’ar za ta cigaba da aiki tukuru don tabbatar da tsaron rayyuka da dukiyoyin dalibai. Amma ana bukatar daliban su rika kiyaye matakan tsaro yayin da suke makaranta.
