Kano: An Zargi Abba Gida-Gida Da Nuna Wariya A Aikin Rusau

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar a ranar Juma’ar nan ne gwamnatin jihar ta ayyana wasu gine-gine a cikin wadanda za a ruguza saboda zargin sun tare badalar garin. A rahoton da Premium Times ta fitar, an ji cewa ana zargin an yi wadannan gine-gine ne a filayen da Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta saida.

Abin mamakin shi ne an tsallake wasu cikin shaguna da sauran ginin da aka yi a filayen da aka saida a lokacin mulkin Rabiu Musa Kwankwaso Ubangidan sabon Gwamna Abba Gida-Gida.

Rahoton ya ce an yi haka tun a gwamnatin farko ta Kwankwaso, amma da Malam Ibrahim Shekarau ya zama Gwamna a 2003, bai rusa gine-ginen mutane ba. Masu zargin gwamnati da son kai sun ce a lokacin Abba Yusuf ya na Kwamishina, an yanka filayen badala daga Kofar Fanfo har zuwa Kofar Kabuga.

Da Ganduje ya samu mulki, sai ya saida fuloti daga Kofar Fanfo zuwa Kofar Nasarawa. A halin yanzu wadannan gine-gine ne gwamnati za ta rusa.

Mukhtar Mudi Sipikin ya zanta da Wakilinmu a kan wannan batu, ya ce gwamnatin Kwankwaso ta yanka filaye, amma ba a tanka su ba. ‘Dan siyasar ya ce a Kantin Kwari, an yi irin haka daga Kofar Mata zuwa Hauren Balagu, haka zalika an saida shaguna a filin wasa da ke Kofar mata.

Abba Gida Ya Yi Makin Shaguna Da Gidajen Mai Na Miliyoyin Naira Cikin Wadanda Za a Rushe Maganar da ake yi, hukumar KNUPDA ba ta da niyyar rushe wadannan gine-gine da shagunan da aka yi kafin Abdullahi Ganduje ya zama Gwamna a 2015.

Idan za ayi afuwa, Sipikin ya na ganin ya kamata gwamnati ta yafewa kowa, muddin ba haka aka yi ba, ya ce za ayi zargin akwai rashin adalci a lamarin. Gwamnati ta na da ikon yin bincike domin hukunta masu laifi a gwamnatin Ganduje, ya kara da cewa bai kamata aika-aikarsu ta shafi mutanen gari ba.

Related posts

Leave a Comment