Kungiyar wakilan gidajen jaridu na ?asa reshen jihar Kaduna (Correspondents Chapel) ta na?a shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Alhaji Sani Liman Kila a matsayin uban ?ungiyar.
Da yake jawabi a wajen taron nadin da ya gudana a ofishin Shugaban ma’aikatan a fadar gwamnatin jihar Kaduna, shugaban kungiyar wakilan ‘Yan Jaridar Alhaji Abdulghaffar Alabelewa yace la’akari da irin kauna da gudummuwa da Sani Kila ke ba ‘yan jarida a fa?in jihar ne ya sa kungiyar ta karrama shi da mukamin uban ?ungiyar.
Shugaban ‘yan jaridar ya ?ara da cewar ‘yan jarida a Jihar Kaduna a yanzu suna gudanar da ayyukan su cikin walwala da natsuwa sa?anin yadda abubuwa suke a baya inda ya bayyana hakan a matsayin kokari na shugaban Ma’aikatan fadar gwamnatin.
A jawabin sa shugaban Ma’aikatan fadar gwamnatin Alhaji Sani Liman Kila ya godewa ?ungiyar ‘yan jaridar bisa ga wannan karramawa da suka yi mishi, inda ya bada tabbacin yin aiki kafada da kafada dasu.
“Yan jarida mutane masu muhimmanci a cikin al’umma wa?anda suna iya bu?ewa da rufewa duk lokacin da suka ga dama, wannan karramawa da suka yi mini ta zama abin alfahari a gareni kasancewata mutum na farko da ya samu irin wannan matsayi, ina baku tabbacin kofofin mu za su kasance a bu?e gareku a kowane lokaci”.
