Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bayyana cewa nadin sabbin shugabannin tsaro da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ya kara kusanta Najeriya zuwa ga ganin karshen matsalolin tsaronta.
Gwamnan ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da daraktan labarai da kula da harkokin labarai na jihar Mamman Mohammed ya gabatarwa manema labarai a Damaturu babban birnin Jihar.
Da yake yaba masa musamman a kan sabon mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, Buni ya nuna karfin gwiwar cewa tsohon shugaban EFCC zai yi amfani da tarin gogewarsa wajen yakar rashin tsaro.
“Malam Nuhu Ribadu ya kasance kwararre wanda zai yi aiki tare da shugabannin tsaro don cimma manufar da aka sanya gaba. “Shugabannin tsaron ma suna da gogewa da karfin gwiwar a Najeriya wajen yaki da rashin tsaro.
