Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da nadin Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya a matsayin sabon sarkin masarautar Gaya.
Wannan ya biyo bayan zabinsa da masu zaben Sarkin masarautar sukayi a jiya Asabar.
Sakataren Gwamnatin jihar, Usman Alhaji, ya bayar da wannan sanarwa a gidan gwamnatin jihar yayinda aka karbi bakuncin masu zaben Sarki.
A Laraba, 22 ga Satumba 2021, Allah ya yiwa Mai Martaba Sarkin Gaya , Alhaji Ibrahim AbdulKadir, rasuwa.
Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin babban hadimin gwamnan Kano kan kafafen yada labaran zamani, Abubakar Aminu Ibrahim.
