Hukumar Zabe Ta Bayyana Dalilin Rashin Sabunta Rijistar Zabe

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce rashin samun sabbin bayanai kan mace-mace a Najeriya ya hana ta cire sunayen matattun ‘yan kasa daga cikin rajistar masu kada kuri’a.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayar da wannan bayanin a lokacin da yake zantawa da Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) Nasir Kwarra, a Abuja a ranar Juma’a, 24 ga watan Satumba.

Don haka, Yakubu, ya bukaci Hukumar NPC da ta tabbatar da samar da bayanan mutanen da suka mutu ga INEC don yiwa rijistan kwaskwarima.

“Wata?ila kuna so ku fara da wadatar da mu da jerin fitattun ‘yan Najeriya da suka mutu, ma’aikatan gwamnati da jama’ar gari wa?anda aka tattara daga bayanan ma’aikatun gwamnati, sassan da hukumomi da sauran ‘yan Najeriya daga asibiti da bayanan jana’iza a duk fa?in ?asar.

“Mun yaba da cewa wannan aiki ne mai wuya amma wannan shine dalilin da yasa muke da Hukumar Kidaya ta Kasa. Muna da yakinin cewa NPC tana da karfin yin hakan. Wannan bayanin yana da mahimmanci ga INEC don ha?aka amincin rijistar masu za?e ta ?asa ”

Related posts

Leave a Comment