Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta samu izinin fara amfani da sabbin jiragen ‘Super Tucano’ wajen ragargazan yan bindiga masu garkuwa da mutane a fadin tarayya.
A shekarar 2021, Gwamnatin tarayya ta sayi sabbin jirage daga kasar Amurka. Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami SAN, ya bayyana hakan a shirin Good Morning Nigeria na tashar NTA ranar Talata.
Gwamnatin tarayya ta samu izini daga wajen Amurka kuma ta yi alkawarin amfani da jiragen yadda ya kamata. Yace yanzu haka ana kokarin sanya jiragen cikin kundin dokokin Najeriya.
“Muna fuskantar matsalar yan bindiga a Arewa maso yamma kuma shi yasa muka sayi makamai wajen yaki da su.” “Mun samu izinin amfani da Super Tucano. Yanzu muna shirin kattabashi cikin doka.”
