Da Yiwuwar PDP Ta Sha Mummunan Kaye A 2023 – George

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Cif Bode George ya gargadi jam’iyyar hamayyar cewa za ta iya shan kaye a zaben 2023 saboda rikicin cikin gida da ya ?i ci ya ?i cinyewa a jam’iyyar.

George, ya yi gargadin cewa PDP tana iya rabuwa biyu Jam’iyyar PDP ta Arewa da Jam’iyyar PDP ta Kudu, idan shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya ki yin murabus kamar yadda aka bu?aci hakan tun farko.

“Bari in fadi karara cewa shugaban jam’iyya na kasa da dan takarar shugaban kasa bai kamata su fito daga yanki guda daya ba wato yankin arewacin kasar.”

Bode George, wanda tsohon sojan ruwa ne ya bayyana hakan ne ga manema labarai a birnin Ikko na jihar Legas kan tasirin siyasar bangarenci da rashin daidaita a jam’iyyar.

Jigon jam’iyyar na PDP ya shawarci Ayu ya cika alkawarinsa na sauka, idan dan takarar shugaban kasa ya fito daga arewa to ya kamata shugaban jam’iyya ya fito daga Kudu, ya koka kan cewa PDP ta saba ka’idar tafiya tare da kowa, domin dan takarar shugaban kasa da shugaban jam’iyya na kasa duk yan arewa ne.

George ya ce zai dace a bawa yankin kudu maso yamma mukamin shugaban jam’iyya na kasa don kada su rika jin kamar an ware su kuma ba a musu adalci ba. Jagoran jam’iyyar ya ce PDP na fuskantar ‘babban hatsari’ da zai iya kawo mata cikas wurin samun nasara a zabe.

Related posts

Leave a Comment