2023: Jonathan Ya Gargadi ‘Yan Najeriya Kan Zaben Tumun Dare

Rahoton dake shigo mana daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar tsohon Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya shawaci ‘yan Najeriya kan irin shugabannin da ya kamata a ce sun zaba a zaben 2023 mai zuwa.

Jonathan ya bayyana wannan batu ne jim ka?an bayan ganawa da tsoffin shugabannin Najeriya biyu na mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdulsalam Abubakar a birnin Minna na jihar Neja.

Da yake bayyana shawararsa, ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su maida hankali su zabi shugabannin da za su yi aiki tukuru don kawo ci gaba a kasar nan, ba shugabannin da za su mayar da hankali wajen cin amanar kasa ba.

Hakazalika, ya ce ya kamata a duba shugabannin masu inganci da kuma tarihi mai kyau don haifar da da mai ido a lokacin mulkinsu domin kauce wa sake afkawa cikin matsalar da ake ciki ba.

Related posts

Leave a Comment