Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa Kannywood, Sani Garba, ya musanta jita-jitar da ake ya?a wa cewa ya mutu a kafafen sada zumunta.
A makon da ya gabata ne akai ta ya?a jita-jitar cewa shahararren jarumin mai wasan barkwanci ya kwanta dama musamman a kafafen sada zumunta.
Sai dai a wani sakon bidiyo da jarumin ya yi, kuma abokin aikinsa a masana’antar Kannywood Abba Almustapa, ya saki a Instagram, Garba yace yana nan da ransa bai mutu ba.
“Ga ni kuna gani a gabanku, ban mutu ba ina nan a raye, amma idan lokaci na ya yi zan mutu, ba sai kun yayata cewa na mutu ba.” “Ina nan ban mutu ba amma idan lokacina ya yi dole zan mutu, kuma ina amfani da wannan dama wajen mika godiya ta ga masana’antar Kannywood baki ?aya bisa ?awainiya da ni.”
“Ina mika godiya ta ga baki ?aya mutanen dake Kannywood, sun kasance masu taimaka mun da ku?i da kuma duk abinda ya dace.”
Jarumin, wanda ke fama da ciwan Suga, ya bayyana cewa yana samun sauki kuma yana cigaba da ganin likita kamar yadda aka umarce shi. Garba SK na ?aya daga cikin jaruman Kannywood masu barkwanci, wa?anda suka jima suna fitowa a fina-finai, kuma a wani lokacin ya fitowa ne a matsayin Uba.
