Dr Shamsuddeen Aliyu mai Yasin Garkuwan makarantar Zazzau daya daga cikin wadanda suka jagoranci Sallar da addu’oin ya shaida wa BBC cewa an gudanar da sallolin ne a filaye Idi da ke cikin Zaria.
Ya ce daruruwan mutane ne suka halarci Sallar da zaman addu’oi domin neman Allah ya yi maganin ?an bindiga wa?anda ya ce sun yi wa garin Zaria kawanya.
“Mun ga cewa ba mu da mafita illa mu koma wa Allah mu tuba domin Ya yi muna maganin wadannan yan bindigar,” in ji shi.
A ranar Litinin aka rufe addu’oi bayan tsawon kwana shida ana yi a kullum.
Ya ce limamin masallacin juma’a na filin mallamawa ne ya jagoranci Sallar da aka yi a masallacin idi na Tudun wada.
A kwanakin baya ne Sarkin Zazzau ya ce ?an bindiga masu satar mutane sun addabi garinsa musamman bayan harin da suka kai suka saci mutane
Bayanai sun ce maharan ?auke da bindigogi ne suka shiga sabuwar unguwar Kofar Gayan inda suka kutsa cikin gidaje suka yi awon gaba da iyalai ciki har da ‘yan mata da samari.
Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da ‘yan bindiga suka sace ?alibai da malamai a Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke garin na Zaria.
