Fashe-Fashen Rumbunan Abincin CORONA: Ya Dace A Nemi Gafarar Sadiya – Zalawah

Da yawan marubuta a shafukan sada zumunta (Social Media) musamman masoya Shugaba Muhammadu Buhari na kira ga dumbin ‘yan adawar Gwamnatin tarayya da wasu da suke ganin tsananin rashin tausayi da karerayin da take ya yi yawa a gwamnatin cewa da su nemi yafiya da kuma gafarar Ministar Iftila’i da kuma jinkai da walwala Hon. Sadiya Umar Farooq.

A kan yawan karyata ta da ‘yan Nijeriya ke yi duk sanda ta ce an turawa jihohi tirelolin abinci don rabawa talakawan Najeriya, har wasu ke kiran ta da suna (Zubaida) don bayyana ta a matsayin makaryaciya.

Sai gashi cikin ‘yan kwanakin nan fusatattun matasa da suka fake da zanga-zangar #EndSARS suna ta fasa rumbunan ajiye wannan tallafin a wasu jihohin kasar nan da suka hada da Lagos, Edo, Ekiti, Jos da sauransu. Wanda hakan ke tabbatar wa duniya cewa ashe dai gwamnatin tarayya na aikewa da tallafin ba karya bane.

Allah ya kara taimakon wanan gwamnati a wuraren da ta gaza, ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa. Amin

Related posts

Leave a Comment