Gombe: Sama Da Yara Dubu 100 Ne Za Su Ci Gajiyar Sabon Shirin Gwamnati

Rahotanni daga Jihar Gombe na bayyana cewar sama da yara da matasa dubu dari dayane zasu ci moriyar wani sabon Shirin gwamnatin tarayya Mai taken yara masu fuskantar barazanar rayuwa.

Shirin dai yana karkashin ofishin mai bawa shugaban kasa shawara ce ta musammam kan inganta walwala, da aka tsara domin tsame yara marasa galihu da almajirai da matasa daga tituna domin a inganta musu rayuwa su.

A jawabinta yayin kaddamar da Shirin a Gombe mai bawa shugaban kasa shawara ta Musammam Maryam Uwais tace shirin wani bangare ne na kokarin gwamnatin tarayya na kebe Yara marasa galihu daga gararanba a tituna kuma jihar Gombe ce jihar farko da aka kaddamar da Shirin a Nigeria.

Maryam Uwais ta bayyana jin dadinta ga gwamnatin jihar Gombe saboda bawa Shirin goyon baya da samar da ofishi don gudanar da Shirin da zai koya wa masu cin gajiyarshi sana’o’i daban-daban.

Dayake jawabi Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ya yabawa gwamnatin tarayya saboda samar da Shirin da yace zai dafawa kokarin gwamnatin shi wurin kyautata rayuwar Yara marasa galihu da matasa, yana mai kira ga masu cin moriyar Shirin da cewa su mai da hankali wurin cin moriyar Shirin dake da manufar kyautata rayuwar su.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya wanda ya bada tabbacin bada goyon bayan gwamnatin shi ga irin wanan Shirin don bawa marasa karfi damar sanin cewar suma ana damawa dasu yace gwamnatin shi ba zatayi kasa a gwiwa ba wurin Samar wa jama’a ribar dimokura?iyya.

Related posts

Leave a Comment