Ministar Harkokin Jin?ai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta ce Gwamnatin Tarayya ta kashe sama da dala biliyan 5 daga shekarar 2016 zuwa yanzu wajen ya?ar fatara da yunwa a ?asar nan.
Ministar ta bayyana haka ne a wajen taron mi?a takardun kama aiki tare da komfutocin duba aiki ga mutum 248 da aka ?auka aikin sa ido kan Shirin Inganta Rayuwa na ?asa (NSIP) a Jihar Adamawa a ?arshen mako.
Hajiya Sadiya ta ce tun tuni Shugaba Muhammadu Buhari ya cika al?awarin da ya yi a cikin 2016 cewa zai yi ?o?arin ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ?angin fatara da yunwa.
Ta ce Shugaban ya yi hakan ta hanyar biyan dala biliyan 1 ga shirin na NSIP domin a rage fatara da kuma tazarar da ke tsakanin mai akwai da mara shi.
Ta ?ara da cewa bayanan da Shugaban ya yi a jawabin sa na Ranar Dimokira?iyya daidai ne, inda ya ce ya yanzu gwamnati ta ceto mutum miliyan 7 da rabi daga ?angin fatara.
Ta ce, “Ina farin cikin sanar da kuwa cewa a kowace shekara daga 2016 lokacin da mai girma Shugaban ?asa ya ?addamar da shirin NSIP, ya bada amincewar a kashe dala biliyan 1 a cikin wannan shirin a kowace shekara (wanda jimillar ta kama sama da dala biliyan 5 kenan).
“Wannan ya na daga cikin ?udirorin da Shugaban ?asa ya ?auka domin cika al?awarin sa na fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga fatara.”
