Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Uwargidar shugaban Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari, ta bukaci hukuma ta yi abin da ya kamata na ganin an kawo karshen matsalar rashin tsaro ta hanyar sake ?aukar wasu sabbin Jami’an tsaro domin babu shakka an shiga wani yanayi a kasar.
Uwargidan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi wannan kira ne a lokacin da ta zauna da matan shugabannin hafsoshin tsaro na kasa a fadar Aso Villa jiya Talata.
Mai taimakawa uwargidan shugaban kasar wajen sha’anin yada labarai da hulda jama’a, Aliyu Abdullahi, ya fitar da wannan jawabi a Abuja a ranar Litinin.
Mai magana da yawun Aisha Buhari ya yi wa jawabin take da ‘Aisha Buhari charges wives of service chiefs.’ Uwargidar ta yi magana a kan abin da ya shafi rawar da mata za su taka wajen cigaban kasa, ta ce ya kamata su ba mazajensu gudumuwar kawo zaman lafiya.
Har ila yau rahoton ya ce Aisha Buhari ta yi amfani da wannan dama ta yi kira ga hukumomi su rika biyan fanshon tsofaffin sojoji da su kayi ritaya a kan kari. Hakan zai zaburar da sauran jami’an da suke aiki a halin yanzu.
