Rahotanni daga Jihar Filato na bayyana cewar ?an takarar jam’iyyar PRP a zaben cike gurbi na maza?ar Bassa/Jos, Muhammad Adam Alkali, yace za su kalubalanci sakamakon za?en da INEC ta sanar a Kotu.
VOA Hausa ta tattaro cewa bayan kammala za?en wanda aka gudanar ranar Asabar a kewayen maza?ar Jos ta arewa da Bassa, hukumar za?e mai zaman kanta (INEC) ta sanar da ?an takarar PDP ya samu nasara.
Sai dai sakamakon za?en ya bar baya da ?ura, inda ?an takarar PRP da ya zo na biyu a yawan Kuri’u ya yi zargin cewa an kulla wata makar?ashiya a wurin tattara sakamakon.
Muhammad Alkali, ya yi zargin cewa akwai sakamakon wasu runfunan zabe da aka kawo daga baya, amma aka ayyana PDP a matsayin jam’iyyar da ta samu nasara.
Haka nan kuma, ya yi ikirarin cewa akwai abubuwan da suka gani a za?en wanda ya sa?a wa dokar ?asa, hukumar zabe da ma yancin ?an Adam. Bisa haka ne, Muhammad, ya lashi takobin cewa jam’iyyarsa ta PRP zata ?alubalanci sakamakon a Kotu, domin nema wa al’ummar maza?ar ?ancin su.
“Akwai abubuwan da muka gani an yi wa?an da suka yi hannun riga da dokokin ?asa, dokokin hukumar INEC da kuma yancin ?an Adam, don haka zamu yi fafatukar kwato wa al’umma hakkinsu a Kotu.”
Idan ba a mance ba, a ranar Lahadi hukumar INEC ta sanar da ?an takarar PDP, Musa Agah, a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 40,343. Baturen za?en, Oyerinde, ya ce hakan ya ba shi damar lallasa abokan takararsa na PRP wanda ya samu kuri’u 37, 754. da kuma na APC, Abbey Aku, mai kuri’u 26,111.
