Katsina: Sarki Ya Amince Da Murabus Din Waziri Lugga

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar mai martaba Sarkin Katsina kuma shugaban majalisar sarakuna ta jihar Katsina, Alhaji Abdulmunini Kabir Usman ya amince da murabus din da Wazirin sa, Alhaji Sani Abubakar Lugga ya yi daga mukamin sa.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwar manema labarai dauke da sa hannun Sakataren majalisar Sarkin, Mamman Ifo da kuma aka rabawa manema labarai.

A cikin sanarwar, masarautar ta ce ta amince da murabus din Shehun Malamin ne biyo bayan bukatar hakan da yayi.

Haka zalika sanarwar ta cigaba da cewa hukuncin murabus din zai fara aiki ne daga ranar Litinin, 28 ga watan Fabreru.

Idan mai karatu zai iya tunawa, Wazirin Katsina, Farfesa Sani Lugga ya rubuta bukatar murabus din na shi ne daga sarautar a kwanan baya biyo bayan wata takardar tuhuma da neman jin ba’asi da masarautar Katsina ta aika masa kan wasu kalaman da yayi a jihar Kwara kan matsalolin tsaron da suka addabi jihar Katsina da arewacin Najeriya.

Related posts

Leave a Comment