Wata babbar kotu a Yola babban birnin Jihar Adamawa karkashin jagorancin Mai shari誕 Mohammed Danladi a ranar Talata ta kori Sanata Ishaku Abbo a matsayin dan takarar Sanatan Adamawa ta Arewa a karkashin jam段yyar APC a zaben bana.
Kotu ta kori Sanata Abbo ne bisa hujjar cewa mazabarsa da ke karamar hukumar Mubi ta Arewa ta kore shi daga jam段yyar.
Mai shari誕 Danladi, ya bayyana cewa Sanata na da nasaba da kudurin da majalisar zartarwar jam段yyar APC reshen karamar hukumar Mubi ta Arewa ta yanke na korar shi daga jam段yyar a ranar 7 ga watan Oktoba 2022.
Kotun ta kuma yi watsi da cewa Sanata Abbo ba shi da hurumin samun wani hakki ko wata gata da aka bai wa 惣an jam段yyar APC.
Ku tuna cewa a ranar 7 ga watan Oktoban 2022 ne shugaban karamar hukumar Mubi ta Arewa ya amince da korar Sanatan kamar yadda kwamitin ladabtarwa na jam段yyar ya bayar.
Kotun ta kuma hana jam段yyar APC da Sanatan ke neman tazarce a karkashinta kar ta amince da shi a matsayin dan takararta, inda ta ce ba zai iya zama dan takarar jam段yyar ba a zabe mai zuwa.
