2023: Masu Tunanin Na Tsufa Sun Yi Kuskure – Tinubu

Labarin dake shigo mana daga birnin Ikko na Jihar Legas na bayyana cewar Babban jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana kansa a matsayin matashi mai jini a jika tare da sukar masu cewar wai ya tsufa ya zama shugaban ?asa a 2023.

Tinubu ya yi furucin ne a daidai lokacin da ake kiraye-kirayen a bai wa matasa damar yin mulki, sakamakon gazawar da ake ganin tsofaffi sun yi wajen jan ragamar mulkin kasar.

Da yake tabbatar da cewar yana da karfin jagorantar kasar, Tinubu ya ce yana da ikon yi wa Najeriya hidima da kuma daukaka kasar, fiye da yadda masu zato ke zato inda ya bukaci a bashi wannan dama.

Ya fada ma magoya bayansa a wani taro da aka yi kwanan nan cewa APC za ta ci gaba da kare ra’ayin yan Najeriya a gida da waje. “Gani a nan tsaye a gabanku…kuma ni matashi ne,” cewar Tinubu yayin da magoya bayansa ke kara masa karfin gwiwa.

Related posts

Leave a Comment