Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da samar da ayyuka, ya ce ba za a iya amfani da ‘hare-haren’ da aka kaiwa wasu sassan kasar ba a matsayin ‘mizani’ na cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta gaza.
Minista Keyamo ya yi wannan jawabin ne a hirar da aka yi da shi a gidan Channels Television a ranar Juma’a.
A cikin yan makonnin baya-bayan nan, munanan hare-hare sun karu a sassan kasar har da babban birnin tarayya, Abuja. A watan Yuli, an kai hari gidan gyaran hali na Kuje a Abuja an kuma kashe wasu cikin jami’an tsaro masu gadin shugaban kasa.
Da ya ke magana kan lamarin, Keyamo ya ce gwamnatin Buhari bata yi alkawarin cewa ba za a samu hare-hare a kasar ba, ya kara da cewa kawai ta yi alkawarin za ta maida martani ne yadda ya dace.
“A makon da ya gabata, an kai wa wadanda ke taruwa a dazukan Abuja hari an fatattake su an kashe su,” in ji shi. “Wannan shine abin da muka yi alkawari, munyi alkawarin za mu mayar da martani.
Ba mu yi alkawarin hari ba zai faru ba. Munyi alkawarin martani. Mun mayar da martani satin da ya gabata, mun kashe su.
“An samu tsaro a Abuja yanzu. Hakan bai sake faruwa ba a dazukan Abuja. Munyi alkawarin daukan mataki kuma munyi hakan. “Mutane su daina firgita juna.
Bari in fada maka wani abu game da yadda yan bindiga ke tunani. Tsorata mutane suke son yi. Tsoratarwa ne iskar da suke shaka. Suna son haifar da firgici. Shine iskar da yan ta’adda ke shaka.
“A aljanna ne kadai – idan mun tafi can ba za a samu hare-hare ba kwata-kwata. Ba mu shiga aljanna ba. Muna duniya ne, dole a samu hare-hare. Mun mayar da martani da ya dace.
“Ana kai hare-hare, ba haka muka so ba, amma ba mizani ne da za a ce gwamnati ta gaza ba. Ana kai hari gidan yari a Amurka. Wurin da ya fi tsaro a duniya, ana tserewa daga gidan yari. “A kasashen yamma, ana kai hari gidan yari.
Ba alfahari na ke da shi ba. Ba hujja na ke kafawa ba. Ina son gyara kallon da wasu yan Najeriya ke yi wa lamarin ne.”
