INEC Ta Tsawaita Wa’adin Rijistar Zabe

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce za a kara wa’adin yin rijistar zaben a fadin kasar baki daya.

Cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter INEC ta ce shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan yayin wani taro da hukumar ta shirya a Abuja.

Kazalika ya yi bayanin kan cewa mutane su guji sayar da kuri’arsu, duk wanda ya yi rijistar za?e ya tabbatar da cewa ya ka?a kuri’u ranar zabe.

Shugaban INEC din ya nuna cewa zaben 2023 zai zama mai tsafta, wanda babu cuta babu cutarwa cikinsa.

Daidaikun mutane da kungiyoyin rajin kare hakkin dan adam dai sun yi ta kiraye-kirayen a kara wa’adin yin rijistar, saboda wadanda ba su yi ba da wadanda ta su ta bata da wadanda ke son a sauya musu wurin yin zaben da dai sauransu.

Related posts

Leave a Comment