Da Dumi-Dumi: Masu Biredi Za Su Tsunduma Yajin Aiki

Kamfanonin biredi a Nijeriya sun yi barazanar tafiya yajin aiki sakamakon ?arin farashin kayayyakin ha?i.

Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito ?ungiyar ‘Association of Master Bakers and Caterer of Nigeria’ wadda ta ce farashin fulawa da sikari da sauran kayan ha?i da ake amfani da su wurin yin biredi duk sun yi tashin gwauron zabi.

?ungiyar ta kuma ?alubalancin gwamnatin Najeriya kan zargin nuna halin ko in kula dangane da wannan batu inda ?ungiyar ta yi barazanar tafiya yajin aiki daga ranar 13 ga watan Yulin 2022.

Ko a kwanakin baya dai sai da aka ?ara ku?in biredi a Najeriya sakamakon ?arin farashin kayayyaki.

Related posts

Leave a Comment