Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo a ranar Asabar, yace zaben abokin tafiyarsa Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 1999 babban kuskure ne da ya tafka da ba zai manta ba har abada.
Obasanjo bya yi wannan tsokacin ne yayin jawabi a garin Abeokuta a wani taron shugabanci da sana’o’in dogaro da kai wanda yayi da zababbun dalibai.
“Ban ce ba na kuskure ba, ina yin su da yawa amma abu daya dake faruwa da ni shine Ubangiji bai taba tozarta ni ba wannan shine abinda yafi muhimmanci”.
“A misali, daya daga cikin kura-kuran da na tafka shi ne zabar na yi lokacin da zan zama shugaban kasa. “Amma saboda kuskure ne mai inganci, Ubangiji ya tsare ni daga shi.”
