Tallafin Mai: Za Mu Kashe Triliyan 6.72 A 2023 – Fadar Shugaban Kasa

Rahotanni daga birnin Tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta ce za ta samar da kudin tallafin man fetur da ya kai naira tiriliyan 6.72 a shekarar 2023

Jaridar The Nation a Najeriya ta ruwaito Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare Hajiya Zainab Ahmed na bayyana haka a Abuja babban birnin kasar ranar Alhamis.

Hajiya Zainab ta ce gwamnati ta kiyasta cewa za ta samar da kudaden ne ta hanyoyi guda biyu kamar yadda yake kunshe a cikin kasafin kudin kasar.

A karkashin hanya ta farko, ministar ta ce ”An kiyasta cewa za a samar da tallafin tiriliyan 6.72 a shekarar 2023.

Ta kuma kara da cewa wadannan kudade kamfanin NNPC ne zai samar da su a madadin gwamnatin tarayya.

Related posts

Leave a Comment