Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar masu Garkuwa da Fasinjojin jirgin ?asan Kaduna/Abuja sun bukaci kudin fansa Naira Biliyan 4.3 a kan naira Milyan 100 kan duk mutum ?aya
Yanzu haka dai akwai ragowar Fasinjojin 43, a wajen yan garkuwar
An sanar da bukatar hakan ga iyalan wadanda aka yi garkuwa da su a makon jiya.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyar bayan da wasu da dama dauke da makamai suka kubutar da wadanda ake zargin sun kitsa garkuwa da su daga gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Kungiyar IS da ke yammacin Afirka ta dauki alhakin kai harin a wani faifan bidiyo da ta fitar bayan sa’o’i 24.
A yayin harin, sama da mayakan Boko Haram 300, wadanda aka yanke wa hukunci da sauran fursunoni, ‘yan ta’addan ne suka arce.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta sanya bayanan kwamandojin Boko Haram 64 a cikin ma’adanar bayanai ta Interpol da suka tsere daga hannunsu a lokacin harin.
