Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki sun bayyana goyon bayansu ga Sanata Kashim Shettima a matsayin ?an takarar mataimakin shugaban ?asa a jam’iyyar a za?en 2023.
Gwamnonin sun bayyana goyon bayansu ne bayan sun gana da Buhari a Daura.
A ranar Lahadi ne ?an takarar shugaban ?asa Bola Tinubu ya sanar da tsohon gwamnan Borno Sanata Kashim Shettima a matsayin wanda zai masa takarar mataimaki.
Shugaban gwamnonin na APC Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu da gwamnan Imo Hope Uzodimma wa?anda suka yi magana a madadin sauran gwamnonin sun ce da yawun bakinsu aka amince da Kashim a matsayin ?an takarar mataimakin shugaban ?asa.
Sun kuma yi al?awalin yin aiki domin tabbatar da jam’iyyarsu ta APC ta yi nasara a za?en 2023.
