Aminu Kano Ya Cika Shekaru 38 Da Rasuwa

Shahararren ?an siyasan a arewacin Najeriya, Marigayi Mallam Aminu Kano wanda ya ri?a fafutukar kar?owa talakawa ?ancin su, Ya rasu ne ranar 17 ga watan Afrilu 1983 a jihar Kano zamanin mulkin Alh. Shehu Aliyu Shagari yana mai shekara 62 a duniya.

Allahu Akbar!

A TA?AICE: Da farko Malam Aminu Kano yana tare da jam’iyyar NPC kafin ya ?alle da jama’ar sa zuwa NEPU. Malam da mutanen sa sun gamu da tsangwama daga manyan NPC a NEPU, A 1954 yayi takarar kujerar majalisa ya sha ?asa hannun Maitama Sule daga baya Aminu Kano samu zuwa majalisar.

Malam Aminu Kano yana cikin manya a majalisa a shekarar 1959. Bayan an kifar da gwamnatin su Sardauna kuma Malam ya ri?e Ministan lafiya na tsawon lokaci a gwamnatin Sojan ta Gowon. A 1978 Aminu Kano yayi takarar shugaban ?asa amma jam’iyyar sa ta PRP ba ta kai labari ba, da shi akai ta gwagwarmaya wajen mayar da mulki ga hannun farar hula azamanin Yakubu Gawon wanda Yakubun ya daga bayar da mulkin wanda adalilin hakan ya haddasa hanbarar da gwamnatin Gawan din a shekarar 1975 inda Murtala Muhammad ya gajeshi.

Dashi akai gwagwarmaya wajen mayar da mulki ga farar hula a shekarar 1979.
Malam Aminu Kano shi ne shugaban jam’iyar PRP kuma ?an takararta na shugabancin ?asa a shekarar 1979.

Yayi ?aurin suna wajen ?in manufofin turawa dama duk wanda zai kawowa arewa wargi, mutum ne wanda bashi da kwa?ayi kuma baya siyasar ku?i face a?ida zalla kawai, Indai ka jiyo muryar shi to akan arewane da talakawa, duk ?ungiyoyin da yayi ko ya jagoranta to gaba dayan su za kuji na Arewa ne, Bayan mutuwar Marigayi Malam Aminu Kano an sakawa muhimman wurare sunan sa kamar irin su filin jirgin sama na Kano wato Malam Aminu Kano Airport da kuma asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano wato Aminu Kano Teching Hospital da sauran su da dama.

Allah yajikan Malam Aminu Kano, Ya Allah kasa mu matasan arewa muyi koyi da irin halayyar wa?annan bayin Allah nagari, wanda komai nasu akan arewa ne, Allah ya jikan Malam Allah Ubangiji ya kai haske kabarin sa, tare da sauran magabatan mu Amin.

Anas Saminu Ja’en
17-4-2021

Related posts

Leave a Comment