Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar, inda ya ya ce ita ce mafi karfi a kasar nan wajen inganta lissafin kudaden jama’a da kuma jagoranci nagari.
Ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro na kungiyar akawun Najeriya (ANAN) wanda aka gudanar a Nassarawa GRA, Kano, a ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba.
Kalaman dai na Ganduje sun haifar da surutai a ?asa ta la’akari da halin da Gwamnan ya ta?a tsintar kanshi a ciki na zargin karbar hanci da rashawa a shekarun baya, amma babu wani mataki da hukumar ta ?auka a matakin jiha.
Duk da yake an ruwaito cewa shugaban Hukumar ya?i da rashawa ta jihar Kano Dr Rimin Gado ya ?alubalanci jama’a da cewar duk wanda ya gabatar da ?wa?kwarar shaida na karbar rashawa da ake wa Ganduje ba kame kame ba, Hukumar zata yi aikin ba sani ba sabo.
