Sabon Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Maniyyata na Jihar Kaduna, Dr Yusuf Yakubu Alrigasiyu, ya sha alwashin ba zai bari yan siyasa da ke gaba da gwamna Nasir El-Rufai, su kawo cikas ga ayyukan Hajji na 2022 a jihar ba.
Kasancewarsa wakilin gwamna a hukumar, Alrigasiyu ya ce zai yi duk mai yiwuwa don tabbatar da ganin an yi aikin hajjin cikin nasara.
Da ya ke jawabi jim kadan bayan shiga ofishinsa a hedkwatar hukumar da ke jihar, Alrigasiyu ya yi ikirarin cewa akwai wasu yan adawa na siyasa da za su fake da duk wani karamin kuskure don sukar gwamnan da shugabannin hukumar.
“Na zo nan ne a matsayin wakilin gwamna don haka ba zan bari ‘yan adawa na siyasa na ciki da waje su kawo cikas ga aikinmu ba. “Irin wadannan mutanen suna jira su ga mun yi kuskure don su soki gwamnan mu ko mu. Ba zan bari hakan ta faru ba,”.
Ya nemi hadin kai da goyon bayan ma’aikatan hukumar domin ya samu nasara a yayin aikinsa, yana mai alkawarin yi wa kowa adalci. Yayin da ya ce ya yi imani da aiki tukuru, ya yi kira ga ma’aikatan su mayar da hankali su jajirce wurin aikinsu.
