Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta ofishin ministar ku?i Hajiya Zainab Ahmad ta dakatar da Akanta Janar na ?asar Ahmed Idris daga aiki.
Wannan na zuwa ne kwanaki ka?an bayan hukumar da ke ya?i da cin hanci da rashawa EFCC ta kama shi bisa zarginsa da almundahana ta naira biliyan 80.
Ministar ku?i ta Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed ce ta dakatar da shi kamar yadda mai ba shugaban ?asa shawara kan fasahar intanet da kafofin sada zumunta Tolu Ogunlesi ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Ya bayyana cewa dakatar da aka yi wa Ahmed Idris za ta bayar da dama a gudanar da bincike na ?warai kan irin zarge-zargen da ake yi masa.
