Yobe: An Cafke Matar Da Ta Hallaka ‘Ya’yan Kishiyarta 4 Da Guba

Rahotannin dake shigo mana yanzu daga Jihar Yobe na bayyana cewa ana zargin wata mata da hallaka ‘ya’yan kishiyarta 4 ta hanyar saka masu guba a cikin shayi.

Lamarin ya faru ne a garin Patiskum na jahar Yobe da ke yankin arewa masu gabashin Najeriya.

A yanzu haka matar na hannun ‘yan sanda kuma tuni suka soma bincike kan lamarin.

Akwai kuma ?a namiji daya da mace biyu kwance a Aassibiti suna jinya.

Maigidan matar Alhaji Haruna ya tabbatar da faruwa al’amarin a wani tattaunawa da BBC, sannan ya ce yanzu haka sun sanar da mahukunta domin daukan mataki.

Kakakin ‘yan sandar Yobe ASP Dungus Abdulkarim ya tabbatar da mutuwar yaran, kuma ya shaida cewa yanzu haka suna kan bincike.

Related posts

Leave a Comment