A yayin da aka fuskanci babban zaben shekara ta dubu biyu da ashirin da uku, an kirayi ‘yan kasuwa dake Arewacin Najeriya da su tabbata sun mallaki katin zabe wanda hakan zai basu damar zaben shugabannin da suka dace wadanda zasu farfado da tattalin arzikin kasan nan baki daya.
Shugaban Kungiyar ‘yan kasuwa dake Arewacin Najeriya Alhaji Muhammadu Ibrahim 86 ne yayi wannan kira a lokacin da yake zantawa da wakilinmu ta waya.
Ibrahim 86 yace ya kamata ‘yan kasuwa kada suyi sakaci wajen yin rijistan katin zabe, don haka yace duk wanda yake da matsala na batan kati ko ya canza anguwa ko kuma gari to yayi kokarin gyara katin zaben akan lokaci wanda a cewar sa da katin ne zai zabe shugaban na gari.
Ya kuma shawarci ‘yan kasuwan da su nesanta kansu daga dukkanin abin da zai kawo tashin hankali a lokaci dama bayan zabe su kuma kaucewa bangan siyasa a duk inda suke domin ganin an samu cigaba yadda ya kamata a fa?in kasan nan baki daya.
86 ya kuma kirayi iyaye da su kasance masu sanya ido akan ‘ya’yansu a koda yaushe domin ganin ba ayi amfani da su wajen bangan siyasaba. Tare da kiran malamai dake wurare daban daban musammanma wadanda ke kasuwanni da su dukufa wajen yin addulo’i domin ganin an kammala harkokin siyasa cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsalaba.
Suma wakilan da zasu yi zaben fidda gwani ya shawarcesu da su kasance masu hada kansu wajen zaben dan takara na gari ba tare da nuna banbancin addini ko kabilanci ba domin ganin an samu cigaban kasa baki daya.
Har wayau Muhammadu 86 ya kirayi ‘yan Najeriya da su hada kansu su cigaba da yin addu’o’i da kuma daina nuna banbancin addini ko kabilanci wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya da kuma kammala zaben shekara ta 2023 lafiya.
