Hajjin Bana: Kimanin Maniyyata 1000 Za Su Rasa Aikin Hajji A Kano

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar kimanin maniyyata 1000, gami da jami’an Hukumar Jin Da?in Alhazai ta Jihar Kano ne za su rasa aikin Hajjin bana sakamakon matsalar rashin jirgin da zai yi jigilar su.

An rawaito cewa tun da fari, Hukumar Hajji ta ?asa, NAHCON ta baiwa kamfanin jirgin sama na Azman Air damar jigilar alhazan Kano, su 2,229 zuwa Saudi Arebiya.

Sai dai kuma Hukumar Jin Da?in Alhazai ta Jihar Kano ta ?i amincewa da jirgin Azman a bisa hujjar cewa bashi da girman da zai kwashi alhazai da yawa a lokaci guda.

Wannan na zuwa ne bayan da a ka jibge alhazan, wa?anda su ka fito daga ?anan hukumomi daban-daban na jihar, a sansanin alhazai tun ranar Asabar ?in da ta gabata ba tare da an kwashe su zuwa ?asa mai tsarki ba.

A Laraba ne kuma Saudi Arebiya za ta rufe shiga ?asar domin aikin Hajji, bayan ta ?ara kwana ?aya a kan ranar da ta sanya za ta rufe bodojinta.

Babban Sakataren hukumar, Muhammad Abba Dambatta, a wata ganawa da manema labarai a ranar Litinin, ya bayyana cewa ya mi?a bu?atar canja jirgin da zai yi jigilar maniyyatan Kano daga Azman zuwa Max Air amma ta ?i amincewa.

A cewar sa, ya zuwa ranar Litinin ?in, mamiyyata 900 da wani abu kacal jirgin Azman ya kai Saudiya a sawu 3, lamarin da ya sanya ya nemi agaji da ga NAHCON, wacce ta yi al?awarin za ta turo jiragen Flynas guda biyu da na Azman guda ?aya domin kwashe dukkan maniyyatan da kuma jami’an hukumar alhazai ta Kano.

A yau Alhamis, rahotanni sun bayyana cewa jirgin Azman ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda ya kwashi alhazai 250 kacal, inda ya bar sama da 1,000 a ?asa, har da Shugaban Hukumar jin da?in Alhazai ta Jihar Kano.

Da yake zantawa da manema labarai a safiyar yau Alhamis, Dambatta, ya ce lamarin ya yi matu?ar sanya shi cikin halin damuwa, inda ya dora laifin a kan NAHCON sabo da “gaza cika alkawarin taimakawa wajen kwashe ragowar maniyyatan na Kano.”

Dambatta ya ce a yau, jirgin AZMAN mai daukar fasinjoji 400 zai tashi daga Kano dauke da maniyyata 250 kacal, inda ya bar sama da Maniyata 940 tare da jami’an hukumar jin dadin alhazai ta jihar.

Dambatta ya kara da cewa Azman Air ya kwashi maniyyata 1,175 a sawu shida sakamakon amfani da suke da ?ananan jiragen da ba su da girman ?aukar maniyyata masu yawa.

Ya ?ara da cewa “wannan ne ya sa mu ka koka kafin a fara jigilar maniyatan aikin Hajji, ganin cewa muna da mafi yawan alhazai, kuma munyi bayanin cewa mun fi son jirgin kamfanin Max Air ya ?auki maniyatan Kano saboda yawan maniyatan da mu ke da su.”

Sakataren ya ?ara da cewa sau 11 ya na zuwa shelkwatar NAHCON da ke Abuja a kan wannan batu, ya ?ara da cewa ya rubutawa hukumar wasi?u sama da 11 don kada a shiga cikin wannan hali, kuma shi ma gwamnan Kano da kansa sai da ya rubuta musu wasika har sau 3 amma abin da aka koka akai sai da ya faru.

Related posts

Leave a Comment