‘Yan fashin dajin da ake zargin sun kaddamar da farmaki akan ayarin motocin shugaba buhari sun bakunci lahira a wani lugudan wuta da rundunar sojojin saman Nijeriya ta kai masu a cikin garin Safana dake jihar Katsina.
Kamar yadda muka samu labari daga majiyar mu cewa bayan harin da yan bindiga suka kai wa Ayarin motocin shugaba Buhari, jirgin ya?in sojojin saman Nijeriya ya yi luguden wuta kan tawagar yan bindiga har sau biyu a jihar ta Katsina.
Mun samu labarin cewa jirgin yakin sojojin saman Nijeriya ya hallaka a?alla yan ta’adda 42 a kauyukan ?aramar hukumar Safana dake cikin jihar Katsina.
Wannan na zuwa ne bayan yan ta’adda sun farnaki Ayarin Motocin Shugaba Buhari tare da bindige mataimakin kwamishinan yan sanda a Dutsin.ma
Majiyar tamu ta sanar mana da cewa wani samame ta sama da Jirgin ya?in rundunar Operation Hadarin Daji ya gudanar ya she?e yan ta’adda 42 a kusa da ?auyukan Zakka da Umadan, ?aramar hukumar Safana a Katsina.
A rahoton da muka samu wata majiya daga cikin jami’an tsaro ta ce jirgin yakin sojojin na tsaka da aikin sintiri, ya samu wasu bayanan sirri cewa anga gittawar wasu yan ta’adda tsakanin ?auyukan Zakka da Umadan inda nan take ya farma yan ta’addan.
Wani Babban Jami’in Soja ya ce nan take jirgin yakin sojojin ya zarce zuwa wurin da aka ba shi bayani, bayan nazari da bincike ya gano inda yan ta’addan suke kilomila 7.1 daga yammacin garin Safana kuma yamma da ?auyen Yartunda.
Ya ?ara da cewa binciken jirgin ya nuna masa wasu mazauna ?auyen na yin takansu yayin da yan bindigan suka farmake su kuma suka shiga gida-gida suka sace wasu.
Ya cigaba da cewa: “Jirgin ya bibiyi yan ta’addan har zuwa ginin da suka ?oye mutanen da suka sato mai nisan kilomita ?aya da sansanin su da suka tattaru, daga nan ne jirgin ya samu izinin sakin wuta.
Bayan nasarar jirgin, mutanen ?auyen da suka gudu lokacin da yan bindigan suka kai musu farmaki sun koma, haka nan wa?an da aka sace sun ku?uta daga wurin da suke tsare. Inji jami’in Sojan
